![]() |
Lafiya Jari ceAuthor: RFI Hausa Language: ha Genres: Science Contact email: Get it Feed URL: Get it iTunes ID: Get it |
Listen Now...
Yadda shirin tallafi ga masu cutar ƙoda zai amfanar da ɗimbin jama'ar Najeriya
Monday, 25 August, 2025
Shirin Lafiya Jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin Najeriya na rage farashin wankin ƙoda ko kuma Dialysis, daga Naira dubu Hamsin ko fiye da haka zuwa Naira dubu 12 kacal. Tuni wannan mataki ya Faranta ran ɗimbin ƴan Najeriya musamman waɗanda ke da ƴan uwan masu fama da wannan lalura da ke da matuƙar cin kuɗi, kodayake murna ta fara komawa jiki, bayan cikakken bayani kan wannan tagomashi ya nuna cewa babu kaso mai yawa na jihohin Arewa maso yammacin Najeriya, duk kuwa da yadda suke da ɗimbin masu fama da wannan lalura. Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin....