![]() |
Najeriya a YauAuthor: Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke aukar hankali a lamuran yau da kullum. Language: ha Genres: News, News Commentary, Politics Contact email: Get it Feed URL: Get it iTunes ID: Get it |
Listen Now...
Yadda Kiristoci Ke Gudanar Da Bikin Kirsimeti A Cikin Musulmi
Thursday, 25 December, 2025
Send us a textA duk faɗin Arewacin Najeriya, ana gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, duk da kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a yawancin yankuna. Kiristoci kan yi bukukuwansu cikin mutunta al’adar Musulmai, yayin da Musulmai kuma ke nuna goyon baya ta hanyar gaisuwa, da tsaro, da mu’amala ta zamantakewa. A wurare da dama kamar Kaduna, Jos, Zaria, Minna da wasu sassan jihar Kano, ana ganin Kiristoci suna zuwa coci ba tare da tsangwama ba, yara suna yin nishadi tare, makwabta suna raba abinci da gaisuwar biki. Wannan yanayi na nuna cewa zaman lafiya, girmamawa da zumunci sun fi bambancin addini ƙarfi a rayuwar yau da kullum ta Arewacin Najeriya.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda kiristoci ke gudanar da bikin kirsimeti a tsakiyar musulmai.













