![]() |
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa. Language: ha Genres: News, News Commentary, Society & Culture Contact email: Get it Feed URL: Get it iTunes ID: Get it |
Listen Now...
Yadda Tattalin Arziki Da Ababen More Rayuwa Suke A Farkon Jamhuriya Ta Hudu Da Kuma Yanzu
Tuesday, 13 January, 2026
A shekarar 1999, lokacin da Najeriya ta sake komawa mulkin farar hula, tattalin arzikin ƙasa da kayayyakin more rayuwa na cikin wani yanayi na dogon mulkin soja. A wancan lokaci, masana da manazarta harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa dogaro da man fetur ya yi wa ƙasar katutu, masana’antu da dama sun tsaya cik, kuɗin ƙasa ya raunana, yayin da rashin aikin yi da talauci suka yi ƙamari. Haka kuma, a cewar manazarta, kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyi, da wutar lantarki, da asibitoci da makarantu sun lalace sakamakon shekaru na rashin kulawa.Yanzu kuma, bayan shafe fiye da shekaru ashirin da biyar da dawowar mulkin farar hula, ra’ayoyin manazarta sun kasu kashi biyu. Wasu na cewa an samu sauye-sauye a wasu fannoni na tattalin arziki da kuma gina kayayyakin more rayuwa, yayin da wasu ke jaddada cewa hauhawar farashi, da karyewar darajar naira, da wasu batutuwa da dama sun cigaba da yiwa kasar katutu.Ko yaya tattalin arziki da kayayyakin more rayuwa suke a lokacin da Najeriya ta dawo mulkin farar huka da kuma wannan lokaci?Wannan shine batun da shirin Daga Larba na wannan makon zai yi duba a kai.









